News

Mazan Kannywood 11 Masu Mabiya A Instagram

Jaruman Kannywood 11 Masu Mabiya A Instagram

Top 11 Most Followed Kannywood Actors On Instagram

Jaruman Kannywood wanda sukafi yawan mabiya a kafar sadarwa ta Instagram, bangaren maza kenan. Kamar dai yanda kuka sani akwai sababbi a masana’antar sannan akwai wanda suka jima a cikinta wanda suka cimma nasarori masu yawa. Na farko dai kusan kowa idan zaiyyi maganar Hausa films dole yasan da Jarumanda zamu nuna muku mabiyansu, musamman Ali Nuhu, Sani Danja,Adamu Zango da sauransu.

Wannan Sune Jerin Jaruma Da Kuma Mabiyan Su Na Instagram.

1. Ali Nuhu

Aliyu Ahmad Nuhu, a cikin su yanada mabiya a Instagram a kalla, mutum miliyan biyu da dubu dari takwas. 2,806,670 wannan jarumi ya taka rawar gani sosai a masana’antar Kannywood (2.8M Followers) Ali Nuhu Haifaffen garin Gombe ne. Wannan shine lissafin shekara ta 2023 komai zai iya sanjawa a shekara ta gaba.

2. Adam A Zango

Adamu Abdullahi Zango, shine yazo ya biyo Ali Nuhu a mabiya a Instagram, akwai wanda suke daidai a yawan mabiya. Adamu Abdullahi Zango yazo na biyu ne a saboda baya kadan ya rasa account dinsa na Instagram hakan ya jawo masa asarar mabiya dayawa a shafinsa na Instagram amma Allah yasa, yasamu nasarar dawo da account dinsa. Yana da Mabiya a Qalla Miliyan Daya Da Dubu Dari Biyar. 1,509,990 qiyasin shekara ta 2023 (1.5M Followers) Adam a Zango ya samu nasarori masa sa adadi a cikin wannan masana’antar.

Sadi Sani Sadiq
3. Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sasiq (SSS) Shine ya samu nasarar zuwa a mataki na Uku Sadiq Sani Babban Jarumi ne a industry na Kannywood yayi manyan fina-finai kamar Sarki, Dan Marayan Zaki, Mati Da Lado, Kalan Dangi da sauransu Sadiq yana daya daga cikin Jaruman da ake alfahari dasu a Kannywood wajen tafiyarda aiki da sauran al’amura. Sannan ya tara mabiya a Instagram 1,508,950 wannan babbar nasara ce sosai dubada da yasamu dayawa daga cikin jarumai a cikin sana’ar. (1.5M Followers)

Umar m shareef Instagram
4. Umar M Shareef

Umar M. Shareef, ya samu nasarar zuwa a na hudu ya biyo bayan Sadiq Sani, Umar M Shareef anfi saninsa a bangaren waqoqin Hausa. Amma ya samu shigo cikin tsarin ne saboda yanda yake fitowa a sababbin fina-finan Kannywood hakan ne ya bada damar jero M Shareef a cikin wannan jerin masu yawan mabiya a Instagram. M Shareef yanada mabiya a Insta a qalla mutum Miliyan daya da dubu dari biyar. 1,507,457 (1.5M Followers).

5. Ado Gwanja

Adamu Isa Gwanja, Shine ya samu nasarar zuwa bayan Umar M Shareef, Gwanja na samu masarori sosai a bangaren waqa da kuma film Ado Gwanja yanada mabiya a Kalla mutum Miliyan daya da dubu dari biyar 1,502,677 (1.5M Followers)

6. Yakubu Muhammad Kumo

Yakubu M. Kumo shine yazo a mataki na shida daga jerin mafiya yawan mabiya a Instagram a cikin jaruman wasan kwaikwayo. Yakubu M. Kumo Ya Jima a cikin wannan ma sana’anta tun yana mawaki har ya dawo jarumi mai fita cikin fina-finai yanada mabiya a kalla Miliyan daya da dubu dari daya da ‘yan kai 1,103,638 Yakubu Muhammad Instagram followers (1.1M Followers)

7. Abba El-Mustapha

Abba El Mustapha, shine yazo a mataki na bakwai Abba El-Mustapha yanada yawan mabiya a instagram El-Mustapha yasamu nasarar samu mabiya a qalla Miliyan daya da’ yan kai. 1,104,358 a Qiyasin shekara ta 2023. Abba El-Mustapha Instagram followers (1. 1M Instagram followers)

 

Nuhu Abdullahi

8. Nuhu Abdullahi

Nuhu Abdullahi, Daya daga cikin manyan jaruman Kannywood, yana taka rara gani matuka a wannan masana’anta ta Kannywood, an samu cece-kuce akan ficewarsa daga shiri mai dogon zango na Aminu Saira (Labarina) Nuhu Abdullahi ya zo a na Takwas a cikin jerin wanda sukafi mabiya a Instagram 1,102,578 (1.1M Instagram Followers) 


9. Sani Musa Danja

Sani Danja sa samu nasarar zuwa a mataki na tara a mafiya yawan mabiya a kafar sada zumunta ta instagram Sani danja ya jima sosai a Kannywood inda yake qarqashin tasa group din wato 2 Effect, Kamar Ali Nuhu dake FKD Production. Sani Danja yanada mabiya a qalla milliyan daya da dauri 1,060,639 Sani Danja Instagram Followers (1M Instagram Followers).

Lawal Ahmad Izzar so
10. Lawal Ahmad

Lawal ya samu nasarar zuwa a mataki na goma a cikin jerin mafiya yawan mabiya a Instagram yanada YouTube BakoriTv wanda yake sake shirinsa mai dogon zango wato Izzar So, Lawan Ahmad ya samu masarori dayawa daga 2020 zuwa yanzu 2023 yanada mabita a instagram a kalla milliyan daya da dauri 1, 054,848 Lawal Ahmad Instagram followers (1M Followers).


11. Ramadan Booth

Ramadan yaro mai tashi Ramadan Yaya ne ga Maryam Booth da Amude Booth. Ya samu nasarori dayawa a wannan masana’anta mai albarka Ramadan yanada mabiya a instagram a kalla dubu dari takwas da sha shida  816,636 Ramadan Booth Instagram Followers (816K Followers)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button