News

Anyi Bikin Fara Aikin Titin Garin Kunji Wanda Sanata Goje Zai Musu

ANYI BIKIN FARA AIKIN TITIN GARIN KUNJI WANDA SANATA GOJE ZAI MUSU

ANYI BIKIN FARA AIKIN TITIN GARIN KUNJI WANDA SANATA GOJE ZAI MUSU

A yau litinin 04/07/2023 akayi bikin fara aikin titin garin kunji dake karamar hukumar Yamaltu Deba wanda mai girma sanata Danjum Goje ya bayar wanda kemanin runfunan zabe 22 zasuci moriyan titin

A yau litinin 04/07/2023 mai girma sanata Danjuma Goje ya aika wakilansa da injiniyoyi don fara aikin titin garin kunji.

Garin kunji dai garine mai tarihi wanda suka shahara a fannin noman rani da na damuna, yana dauke da dubban mutane, saidai suna shan wahala wajen zuwan yaransu makaranta da kuma fito da kayan anfin gona zuwa kasuwanni ta sakamakon rashin hanya da suke fama dashi a garin, idan damuna tayi nisa mota baya shiga garin, ko da mashin mutun zai shiga garin sai ransa ya baci sakamakon rashin hanya.
ANYI BIKIN FARA AIKIN TITIN GARIN KUNJI WANDA SANATA GOJE ZAI MUSU
Al’umman garin sunyi tururuwa manyansu da yaransu wajen zuwa gun biki bude aikin don nuna farincikin na samun wannan titi.

Dayake jawabin shugaban kungiyar nemo cigaba na garin Kunji Muh’d Yaya (Dan Majen Kunji) yace jiya basu iya bacci ba don farinci da aikin, sakamakon idin ana ruwa sama basa iya fidda mara lafiya zuwa asibiti tsabar munin hanyan nasu, amma yan mai girma sanata ya fiddasu a wannan ukuban.

Mai girma sanata ya samu wakilcin Alh Danjuma Babayo da rakiyan Hon Sadiq Kurba, Alh Tanimu Usman Deba, Alh Garkuwa Basambo da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukuman yamaltu Deba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button