News

Hon Mahmud Abdulkarim I. Tumfure Yakai Ziyara, GDJSS Tumfure

Tunfure secondary school gombe

HON MAHMUD ABDULKARIM IBRAHIM TUMFURE YAKAI ZIYARA MAKARANTAN GDJSS TUMFURE

Ayau alhamis
30/June/2022
1st/zhul-hajji/1443

Tsohon Dan takaran kujeran majalisan jiha ayankin Akko North GONA akarkashin Jam’iyyar PDP.

HON COMRD MAHMUD ABDULKARIM IBRAHIM TUMFURE.

Yakai ziyaran gani da ido makarantan GDJSS TUMFURE Wanda take kan hanyan zuwa gidan dakachi, yakai ziyaran ne sakamakon irin halin da makarantan ta tsinci kanta Wanda duk wani mutum me kishin al’umma idan yagani seyatausaya wa dalibai da malaman wannan makarantan,
kadan daga cikin matsalolin makarantan sunhada.

1. Rashin kujerun zama Wanda har ya kaiga dalibai suna Zama akan floor suna karatu.

2. Karancin dakin karatu wato ajijjuwa Wanda dalibai suna Zama har gaban Allo malami seya zallake kafafun dalibai sannan yashiga inda yakeson yayi rubutu akan Allo.

3. Rashin office din zaman malamai
4-Rashin bandakai Wanda idan antashi daga makarantan wasu mutane ke zuwa lungunan ajijjuwa suna yin kashi,
5-Rashin katanga, zakaga mashuna da motoci suna wucewa ta kopar ajijjuwan dalibai.

Wannan shine babban dalilan dayasa HON COMRD MAHMUD ABDULKARIM IBRAHIM TUMFURE yakai wannan ziyaran, ayayin ziyaran yagana da vice principal, senior staff da sauran manyan malaman makarantan inda Suma suke bayyana alhinunsu da rashin jindadinsu akan wannan halin da makarantan takeciki.

Bisaga la’akari da makarantan na gomnati ce HON MAHMUD ABDULKARIM IBRAHIM TUMFURE yabi duk wani tsari dayakamata abi domin ganin ziyaran be bar baya da kuraba, yaruba ingantacciyar wasika wa commissioner of education ta hannun principal da chairman P.T.A sannan yayi alkhawarin inde suka bashi dama zeyi kujerun Zama wa dukkanin ajijjuwan makarantan.

Matemakin shugaban makarantan Wanda yawakilci shugaban makarantan wato principal da sauran malamai sun nuna farincikinsu sosai bisa nuna damuwa dakuma Kawo dauki ga wannan makarantan dashi tsohon dalibin makarantan yayi wato COMRD Mahmud Abdulkarim Ibrahim, sannan sunyi alkawarin cewa zasuyi dukkanin me.

MORE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button