Music

Naziru Sarkin Waka – Katin Zabe Na (Nazir M Ahmad)

Naziru Wakar Katin Zabe Sarkin Waka Naziru Sarkin Waka – Katin Zabe Na (Sabuwar Wakar Naziru)

Nazir M Ahmad, wanda akafi sani da Naziru Sarkin Wakar Sarkin Kano, ya saki sabuwar waqar sa mai taken Katin Zabe Na. PVC, yana kara nusarda mutanen kasar nan. Mahimmancin katin zabe (Voters Card) ya kamata ko wanne dan Nigeria ya mallaki katin zaben sa. Domin ana wanke tukunya ne don girkin gobe,bayan sake wakarsata, Sai mun bata wuta.

Sai Mun Bata Wuta, wakace wanda Naziru Sarkin Waka yayima. Mai neman takarar kujerar shugaban qasa a Jam’iyyar PDP. Wanda wakar ta shiga kunnen Al’umma da dama. Sanna yanzu yazo da wakarda batada wani bangare na Party. Wakar ta karkata ne yiwa al’ummar Nigeria tuni (remembrance) akan mahimmancin katin zaben shekara mai zuwa.

Wannan yun kuri, ne na wayar da kan mutanen arewacin Nigeria akan wannan al’amarin. Ya kamata duk wani wanda yasan ciwon kansa sannan bai gaza shekara sha-takwas bah ya mallaki nasa katin, hakan ne zai bama kowa damar zaben shugabanni da ransu ke so. A tsaya ayi zabe sannan a zabi chan-chanta saboda idan babu kai akwai ‘Ya’ yanka idan babu su akwai iyayenka.

Firgici na qara shiga zukatan mutane, sabida rashin tsaro. Rashin tsaftaceccen muhalli. Talauci (Poverty) ta ratsa ko ina sannan ga rashin aiki ga matasa, da karshe Allah bamu shugabanni na gari ya bama kasa zaman lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button