News
NEWS: Tayi Kira , Akan Tabarbarewar Ilimi a Yankin (Tumfure)
TUMFURE FIRST, ITANE TUSHENMU
Tabbas Abun Takaici Ne Da Bakin Ciki, Kuma Abun Tausayine Idan Aka Duba Halinda Makarantu Ke Ciki A Anguwar Tumfure. Yara Kannenmu Masu Tasowa Basuda Wani Gobe Wanda Yawuce Su Samu #Ilimi Abun Tausayine Kuma Abun Kunya Ga ‘Yan Siyasa Da Suka Bar Wannan Makarantu A Halin Rashin Kulawa, Wanda Sai Lokacin Zabe Yayi Zasu Waiwayo Al’umma.
Tumfure Ba Karamin Koma Baya Ta Samu Bah, Tundaga;
1. Ilimi
2. Kiwon Lafiya
3. Ruwan Sha Da Sauransu.
Muna Kira Da Babban Murya Ga Gwamnati Da Dukkan ‘Yan Siyasa Na Yankin Gona, Dasu Duba Wannan Lamari Domin A Samawa Yara Masu Tasowa Ingattacen Ilimi.
Al’umma Sune Gwamnati, Muna Rokon Allah Yasa Sakon Mu Ya Isa Ga Mahukunta.
©TYAI Media Team