Music

Mai Art – Akori Yunwa (Wakan Siyasa)

Mai Art - Akori Yunwa (Wakan Siyasa)

Mai Art – Akori Yunwa (Wakan Siyasa)

Shahararriyar wakan nan wadda take tashe yanzu wanda sananen mawakin siyar nan na jihar Katsina ya rera wato Mai Art kuma shugaban gamayyar mawakan PDP na jihar Katsina. Mawakin yayi nazari akan halinda qasar Nigeria ke ciki dakuma Jiharsa ta Katsina inda yayi nazari akan hanyoyinda ya kamata a bulloma al’amura da kuma matsalolinda ke damun mutanen kasa baki daya.

Mai Art, yayi nazarin Yunwa na damun talakawan Qasar da kuma yunwa. Inda yake jan hankalin mutane domin su nutsu suyi zabi mai kyau a gammanin zaben 2023 dake qaratowa. Kowa yanada damar zaben wanda zai jogorance sa, bugu da qari mawakin ya tallata gwanayen sa wanda yake gani kamar su zasu cire masa kitse a wuta.

Mawakin ya karkata akalar waqarsa da kuma jan hankalinsa zuwa ga Jam’iyar PDP (People Democratic Party) wanda itace Jam’iyar adawa Nigeria, PDP na kan gaba wajen ganin ta karba mulkin gida da kuma mulkin Kasa baki daya.

Mawakin ya bayyana cewa nagartar su shinr yasa ya rera wannan waka da kuma chan-chanta. Baya kadan anyita samun hatsaniya a tsakanin yan takara da kuma kudancin kasar a Jam’iya mai mulki, akan zaben matakin fidda gwani na shugaban kasar.

Matsalar kasar kullum qara hauhawa take izuwa wani mataki, ga rashin tsaro, rashin kulawa ga dalibai a makarantu, ma’aikata sunata shiga yajin aiki (strikes) rashin kulawa ga marasa lafiya dake kwance a asibitoci. Hakan ne yasa PDP suka zage dantse dan gani mulki ya dawo hannuta. Mai Art yayi amfani da wannan dama domin ganin ya wayarwa mutane kai a matsayinsa na dan kasa wanda keda cikakkiyar dama.

Yau mukai nasarar dora muku wakar a wanan shafin namu wato akori yunwa da rashin tsaro wanan waka anjima ana tsimayin a ina za a  sameta to masha allah yau gata nan mun dora muku ita a wanan shafin namu mai albarka.

Zaku iya tuntubar mu ta wanan number whatsapp domin kuma a tallata muku wakokinku +2348135882889

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button